Shugaba Vladimir Putin na Rasha zai karbi bakuncin takwaransa na China Xi Jinping, wanda zai kai ziyara kasar a mako mai zuwa.
Gwamnatocin Beijing da Moscow sun bayyana cewa shugabannin biyu za su tattauna game da muhimmancin hadin gwiwa, kana za su rattaba hannu kan wasu muhimman yarjejeniyoyi.
- Bakuwar cuta ta yi ajalin mutum 5 a Tanzania
- Yadda jadawalin kwata final na Champions League ya kasance
Bayanai sun ce rabon Shugaba Xi da kai wa Rasha ziyara tun a shekarar 2019.
A ranar Litinin mai zuwa shugabannin biyu zasu hadu yayin wata liyafar cin abinci, inda washe gari za su fara cikakkiyar tattaunawa.
Taron manyan shugabannin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Beijing ta ke kokarin bijiro da wasu muhimman tsare-tsare guda 12 wadanda ake sa ran za su taimaka wajen kawo karshen yakin Ukraine.
To sai dai matsayar da China ta dauka na rashin cewa uffan game da yakin wani abin tambaya ne, kansancewa gwamnatin Beijing na ci gaba da karfafa huldarta da Moscow.
Wasu rahotanni sun ce ana sa ran Shugaba Xi zai tattauna da kafar bidiyo da Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine bayan kammala ziyararsa a Moscow, koda yake har yanzu ba a tabbatar da hakan ba.
A baya-bayan nan dai China ta bukaci Ukraine da Rasha su gaggauta gudanar da zaman tattaunawar sulhu domin kawo karshen tashin tashina da ke tsakanin Kasashen biyu, inda Ukraine ke cewa kiran ya tabo batun samawa iyakokinta martabarsu.
Yayin zantawarsu ta wayar tarho Ministan harkokin wajen China Qin Gang ya fada wa takwararsa na Ukraine Dmytro Kuleba cewa, China na sa ran bangarorin biyu su yi hakuri da juna, su kuma mayar da wukan su kube, tare da amincewa da gudanar da zaman tattaunawar sulhu.
Kazalika Qin ya ce matsayar China daya ce game da rikicin Rasha da Ukraine, wato goyon bayan kudurin gudanar da tattaunawar sulhu wanda ake sa ran ya zama silar kawo karshen yakin da aka shafe sama da shekarar daya ana gwabzawa.
Wannan ne karon farko da China ke yin kira a hukumance tun bayan ministan harkokin wajen Kasar ya soma aiki a cikin watan Disamban shekarar bara.
Kasashen yammacin duniya sun caccaki China a kan rashin caccakar Rasha na yin mamaya a Ukraine, wanda ko a cikin watan da ya gabata Chinan ta musanta zargin da Amurka ta yi mata na yunkurin taimakawa Rasha da makaman yaki.
A makon jiya ne dai Majalisar Dokokin China ta sake zaben Shugaba Xi a wani sabon wa’adi na uku na tsawon shekaru biyar.