✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobarar bututun mai ta kashe mutum 10 a Ribas

Mutanen da suka mutu, lamarin ya rutsa da su ne lokacin da suke kokarin satar mai.

Akalla mutane 10 ne aka tabbatar sun mutu, sakamakon fashewar bututun mai da aka dasa ba bisa ka’ida ba a Jihar Ribas.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a yankin Rumuekpe, a cikin Karamar Hukumar Emaukacin ta jihar.

Kakakin ’yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ya ce har yanzu ba a tantance mutanen da suka mutu ba.

Sai dai binciken jami’an tsaro ya gano cewa, mutanen da suka mutu, lamarin ya rutsa da su ne lokacin da suke kokarin satar mai.

Motoci biyar ne da kuma babura masu kafa uku (Wato Keke NAPEP) guda hudu ne suka kone kurmus.

Satar danyen mai da kuma bude haramtattun matatun mai sun zama ruwa dare a yankin Neja Delta, duk da kokarin da gwamnatin kasar ke yi na magance matsalar.

NAN