✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta tashi a Fadar Shugaban Kasa

Gobara ta tashi a Fadar Shugaban Najeriya ta Aso Rock da ke Aduja. Babban Mai Taimaka wa Shugaban Kasa kan yada labarai Garba Shehu shine…

Gobara ta tashi a Fadar Shugaban Najeriya ta Aso Rock da ke Aduja.

Babban Mai Taimaka wa Shugaban Kasa kan yada labarai Garba Shehu shine ya tabbatar da haka.

Ya ce gobarar ta Fadar Shugaban Kasa ta tashi ne sakamakon matsalar wutar lantarki a ranar Alhamis.

A bayanin da ya yi da safiyar Juma’a,  Shehu ya ce gobarar ba ta yi tsanani ko barna ba sosai.

“Gobarar ta tashi ne a cocin fadar gwamnati sakamakon tartsatsi da kayan lantarki suka yi.

“Amma daga baya kuma jami’an kwana-kwana sun kashe wutar,” inji shi.

Garba Shehu ya kuma tabbatar da cewa ba a sami wata asara me yawa mai yawa ba sakamakon gobarar.