Kayayyaki na miliyoyin Naira sun kone bayan wata gobara ta tashi a fadar Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouq Umar.
Rahotanni sun ce wutar ta tashi ne wajen misalin karfe 4:00 na yammacin Litinin kuma ta shafe sa’o’i tana ci, sai da cinye kusan komai a bangaren da dan Sarkin, kuma Danburan na Daura yake.
- Yanayin kasuwa ne ya sa man fetur ya kara tashi — NNPC
- Mai sana’ar POS ya sha guba saboda bashin miliyan 1.7
Basaraken dai, Alhaji Muhammadu Daha Umar Farouq Umar, shi ne Hakimin Baure.
Rahotanni sun ce ba a sami asarar rai ba, saboda matar basaraken, wacce ’ya ce ga marigayi Sarkin Daura, Muhammadu Bashar, ta yi tafiya lokacin da lamarin ya faru.
Majiyoyi sun ce, “Ko tsinke ba a dauka ba a sashen da gobarar ta tashi, amma dai ba a sami asarar rai ba.
“Muhimman abubuwa da dama ne suka kone ciki har da muhimman takardu,” in ji majiyar.
Da yake tabbatar da lamarin, Kakakin masarautar, Sarkin Labaru Usman Yaro ya ce kodayake ba a kai ga tantance musabbabin gobarar ba, amma ba za ta rasa nasaba da wutar lantarki ba.
Sai dai ya gode wa jami’an kashe gobara da ma jama’ar ta Daura da suka taimaka waen kashe wutar.