✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai sana’ar POS ya sha guba saboda bashin miliyan 1.7

Alkalin kotun ya bayar da umarnin sayar da gidansu don biyan bashin

Wani matashi a Yola, babban birnin Jihar Adamawa, ya yi yunkurin hallaka kansa ta hanyar shan guba kan bashin miliyan 1.760 da ake bin sa.

Umar Faruk Usman, mai sana’ar POS a Karamar Hukumar Yola ya sha maganin kwari ne a cikin kotun da abokinsa, Mustapha Baraya, ya kai kararsa.

Baraya ya bai wa Umar kudi Naira miliyan 1.960 don yin sana’ar POS, amma ya barnatar da su, inda kawai Naira 150,000 aka samu a wajensa.

Duk da kokarin abokin nasa na ganin ya dawo da ragowar kudin ya ci tura, Umar ya ci gaba da yaudararsa, wanda hakan ya sa ya maka shi a kotu.

Kotu ta bai wa Umar umarnin mayar masa da kudin cikin wata guda, amma ya kasa dawo da su bayan cikar wa’adin.

Wanda ake karar da mahaifinsa sun yi alkawarin suna da gonar shinkafa kuma idan suka girbe ta za su biya bashin da ake bin matashin.

Sai dai wasu rahotanni sun ce sun girbe gonar a boye tare da sayar da amfanin gonar.

Wannan dalili ya sanya kotun bayar da umarnin sayar da gidan mahaifin matashin mai sana’ar POS don biyan abokin nasa kudinsa.

Don nuna rashin jin dadin kan hukuncin kotun, Umar ya dauki maganin kwari ya sha a ofishin alkalin da nufin hallaka kansa.

Ya fadi nan take tare da fita daga hayyacinsa, lamarin da ya sanya aka garzaya da shi asibiti don ba shi kulawar gaggauwa.