✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta tashi a Babbar Kasuwar Katsina

Wutar da ta tashi da safiyar Litinin na kan ci kuma ta lakume dukiyoyi.

Gobara na ci gaba da ci a Babbar Kasuwar garin Katsina, Jihar Katsina.

Gobarar wacce ke ci tun da safiyar Litinin ta jawo asarar dukiyoyi na miliyoyin Nairori.

Zuwa yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba, amma wakilin Aminiya ya rawaito cewa kusan ilahirin shagunan da ke bayan bankin Unity da ke cikin kasuwar sun kone kurmus.

Yadda wasu ‘yan kasuwa ke kokarin kwashe kayayyakinsu bayan tashin gobarar.
Yadda shaguna ke ci gaba da konewa a kasuwar.

Har zuwa hada wannan rahoton dai ma’aikatan kwana-kwana na ci gaba da kokarin kashe wutar da wasu majiyoyi ke cewa ta tashi ne a bangaren masu injin nika da kayan abinci.

Wani bangare na kasuwar da ya kone.
Yadda gobarar ta kone wasu shaguna kurmus a Babbar Kasuwar Katsina
Cincirindon jama’a a yayin da jamia’n kwana-kwana suke kokarin kashe wutar.