Wata gobara da ta tashi cikin dare ta yi sanadin konewar shaguna sama da 20 tare da lalata dukiyar miliyoyin kudi a kasuwar Sango-Oju Irin da ke Karamar Hukumar Ibadan ta Arewa a Jihar Oyo.
Aminiya ta ruwaito cewa, wannan shi ne karo na uku da gobara ke tashi a birnin, tun bayan shigowa sabuwar shekara.
- ’Yan bindiga na neman 40m kudin fansar matar basaraken Kwara
- Boko Haram Ta Kashe Magina Ta Sace Mafarauta A Yobe
A baya-bayan nan gobara ta tashi har kashi biyu a sassa birnin daban-daban, lamarin da ya kai ga asarar duniya mai tarin yawa.
Kansila mai wakiltar Ibadan ta Arewa, Oluwayemisi Adeagbo, ya tabbatar da cewa ba a rasa rayuka ba.
Shugaban kasuwar Sango Oju Irin, Alhaji Azeez Mustafa, ya yi kira ga gwamnati da ta tallafa wa ‘yan kasuwar da abin ya shafa.
Ya ce lamarin ya yi muni matuka, duba da yadda yanayin tattalin arzikin da kasar nan ke ciki.
“Gobarar ta faru ne a sakamakon matsalar wutar lantarki. Yawancin ‘yan kasuwar da abin ya shafa sun riga sun tashi. Jama’armu da yawa bashi suka ci don kara jari duba da yadda hauhawar farashin kayayyaki ke karuwa kullum.
“Muna kira ga gwamnati da ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su taimaka domin kada asarar da aka yi ta haifar da matsala ga wadanda abin ya shafa,” in ji shi.