Gobara ta kone wasu sassan kasuwar garin Kiyawa da ke Jihar Jigawa, inda ta lalata rumfuna da dukiyoyi masu tarin yawa.
Kakakin Hukumar Tsaro ta Sibil Difens Adamu Shehu ne, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
- NAJERIYA A YAU: Yadda ‘Yan IPOB Ke Shirin Hana Zabe A Kudancin Najeriya
- Ronaldo zai rattaba hannu da kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya a farkon watan Janairu
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, hudu ga watan Disamba 2022, da misalin karfe 11:15 na safe a kasuwar.
Adamu ya ce gobarar ta lalata rumfunan kasuwar sama da 20 da wasu kayayyaki da darajarsu ta kai ta miliyoyin Naira.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba.
Sai dai shaidun gani da ido sun ce gobarar ba za ta rasa nasaba da wani juji da ke kusa da kasuwar da ake kone shara ba.