✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta kona kasuwar hatsi ta Pataskum

Gobara ta tashi da misalin karfe uku na dare inda ta kone babbar kasuwar hatsin garin Pataskum a Jihar Yobe. Shaguna da dama na kayan…

Gobara ta tashi da misalin karfe uku na dare inda ta kone babbar kasuwar hatsin garin Pataskum a Jihar Yobe.

Shaguna da dama na kayan abinci ne suka kone kurmus a gobarar wadda bayan ta kama ne jami’an hukumar kashe gobara suka hanzarta zuwa kasuwar domin shawo kan wutar inda abokan aikinsu na garin Nangere suka kawo musu dauki.

Wani mai shago a kasuwar mai suna Alhaji Abubukar, da ya shaida wa wakilinmu cewa cikin dare aka kira shi a waya cewa kasuwarsu ta kone, inda nan take ya hanzarta don gane wa idonsa.

Ya ce yana zuwa ya tarar shagonsa ya kone kurmus da buhu 100 a ciki na wake da masara da gyada da abincin dabbobi.

Shi ma wani da gobarar ta shafa Alhaji Danlami, cewa yayi shi ma ya tafka mummunar asara na kayan buhuna da injin matsa da sussuka.

Daga nan sai suka roki gwamnati da ta kawo musu dauki na irin asarar da sukayi, ana kuma kyautata zaton musabbabin gobarar daga wutar lantarki ne

Idan dai za’a iya tunawa babbar kasuwar Nguru ma a jihar ta Yobe an samu irin wannan gobarar a kasa da makonni biyu da suka gabata.