Adadin mutanen da suka rasu a gobarar da ta tashi a wani bene a kasar Afirka ta Kudu sun ƙaru zuwa 74.
Hukumomin agaji a kasar sun ce wasu mutum 200 sun samu kuna da wasu raunuka ciki har da wadanda numfashinsu ya sarke shakamakon shafar hayakin gobarar da ta tashi tun kafin wayewar garin Alhamis.
- Brice Nguema: Wane ne sabon shugaban mulkin sojin Gabon?
- NAJERIYA A YAU: Mece ce makomar Kwankwaso a siyasar Najeriya?
“Mutum 64 ne aka tabbatar sun rusu, ciki har da kananan yara bakwai,” ciki har da dan kasa da shekaru biyu, in ji kakakin hukumar agajin gaggawa ta kasar Robert Mulaudzi.
Ya bayyana cewa an kai wadanda suka samu ranun asibiti, kuma jami’an kwana-kwana na kokarin shawo kan gobarar.
Ana fargabar adadin wadanda suka mutu zai iya karuwa, kuma kawo yanzu dai ba a sanar da musabbabin gobarar ba.