✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Gobara ta kashe mutum 6, wasu 17 sun jikkata a birnin Valencia

An ceto akalla mutum 25 daga gidan da wutar ta tashi.

Hukumomin kashe kobara a kasar Spain sun tabbatar da mutuwar mutum shida, yayin da wasu 17 suka ji raunuka sakamakon tashin wata gobara a Jihar Valencia da ke kasar.

Hukumar Kashe Gobara ta yankin Valencia ta ce wutar ta fara tashi ne tun a yammacin ranar Talata har zuwa wayewar garin ranar Laraba.

Lamarin ya faru ne a wani gari mai suna Moncada mai nisan kilomita 12 daga cikin garin Valencia.

Shugaban Hukumar Kashe Gobara na Valencia, Jose Basset, ya ce wutar ta fara ci ne daga wani bangare na wani gida, inda ta cinye wani daki, wanda a nan aka fara samun gawar mutum biyu.

Kazalika, ya shaida wa manema labarai cewar an ceto mutum akalla 25 daga cikin gidan mai hawa biyu da wutar ta tashi a ciki.

Basset ya kara da cewa ana zargin kayan wutar lantarki ne suka haddasa tashin gobarar.

Shugaban kasar Spain, Pedro Sanchez, ya wallafa sakon ta’aziyya a shafinsa na Twitter ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma jajanta wa wadanda suka ji rauni.