✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta kashe mutum 32 a jirgin ruwa a Bangladesh

Sama da mutum 100 sun samu rauni bayan tabbatar da mutuwar mutum 32.

Hukumomin Kasar Bangladesh sun ce akalla mutum 32 ne suka rasa rayukansu sakamakon wata gobara da ta tashi a wani jirgin ruwa mai dauke da mutum 500.

Wani dan sanda a yankin Barisal, mai suna Moinul Islam, ya ce jirgin ruwan ya kama da wuta ne yayin da yake tsakiyar teku, kuma tuni aka gano gawar mutum 32.

Islam ya ce yawancin wadanda suka mutu wuta ce ta yi ajalinsu sai kadan kuma da suka mutum sakamakon fadawa a ruwa da suka yi.

Kazalika, ya ce ana zargin wutar ta tashi ne daga sashen injin jirgin, daga bisani ta mamaye wasu sassa na jirgin bayan gaza kashe ta da aka yi.

Jami’in, ya ce sun kai mutum kusan 100 da ke cikin jirgin zuwa asibiti saboda konewar da suka yi domin yi musu magani a Barisal.

Wannan na daga cikin hatsari na baya-bayan nan da aka gani a kasar wadda ke bakin teku, yayin da wasu ke danganta hadurran da ake samu da rashin ingancin jiragen da ake amfani da su a kasar.