✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta hallaka magidanci da iyalansa biyar a Gombe

Wata gobara da ta tashi cikin dare a Unguwar Alkahira kusa da Babadidi a Gombe fadar Jihar Gombe ta hallaka wani magidanci da matarsa da…

Wata gobara da ta tashi cikin dare a Unguwar Alkahira kusa da Babadidi a Gombe fadar Jihar Gombe ta hallaka wani magidanci da matarsa da ’ya’yansa hudu, inda ’yarsa mai shekara tara ta tsira.
Wani makwabcin mamacin mai suna Alhaji Abubakar Gani da suke zaune gida daya ya shaida wa Aminiya cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 11:00 na dare suna barci sai ’yar marigarin mai suna Sadiya ta buga masa kofa tana cewa Baban Rahama wuta a dakin Mamana kuma Babana da Mamana suna ciki.
Ya ce a lokacin da ya fito shi da matarsa sun dauki ’ya’yansu biyu suka kai gidan makwabta suna tafiya yana kwalala cewa gobara, inda jama’a suka taru don ceto makwabcinsa da iyalansa, amma lamarin ya faskara saboda hayaki ya turnuke dakinsu ga kuma wuta.
Alhaji Abubakar Gani, ya bayyana Tajudeen da cewa mutumin kirki ne wanda tunda suke zaman haya a gidan babu wani abu na bacin rai da ya taba shiga tsakaninsu haka ma matansu sun zama kamar ’yan uwan juna.
Sadiya mai kimanin shekara tara ta shaida wa Aminiya cewa cikin dare gobarar ta kama dakin Mamarta da ’yan uwanta hudu a cikin dakin wadanda dukansu Allah Ya karbi rayukansu.
Sadiya da ke aji hudu a Firamaren Model da ke Gombe, ’yan uwanta da suka rasu su ne kannenta, Abdurrazak da Isma’il (Abul) da Yasim da yayanta Abdulmalik.
Wani makwabcin gidan mai shagon tireda ya ce an aiko Sadiya ta sayi kyandir a wurinsa da daddare bayan an dauke wuta, wanda bisa ga alamu kyandiri din ne ya yi sanadiyar gobarar.
Malam Abubakar Gani da matarsa Mariya Hambali da ’ya’yansu Rahma da Ramlat da Sadiya ne suka tsira daga gobarar, wadda ta kone gidan kurmus babu abin da aka cire.
Kakakin Hukumar ’Yan Kwana-Kwana ta Jihar Gombe Haruna Wamba, ya tabbatar da faruwar gobarar inda ya ce kyandir ne aka kunna kuma barci ya dauke su har ya ci ya cinye kayan da ke dakin
sannan hayaki ya turnuke su a dakin suka gagara fita. Ya ce amma ’yar marigayi ta fito ta yi ta kwalala cewa gobara ta kama dakinsu amma duk da haka kwanansu ya kare.