Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani yaro mai kimanin shekara hudu mai suna Abubakar Sani, sakamakon gobarar da ta tashi a Yakasai, Layin Inuwa mai mai a Karamar Hukumar Birnin Kano.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi ne ya bayyana hakan a Kano.
- An kama likita bisa zargin sace jariri a Abuja
- Yadda wasan Najeriya da Afirka ta Kudu ya yi ajalin mutum 5 saboda faɗuwar gaba
Saminu ya bayyana cewa, hukumar ta samu kiran gaggawa daga ma’aikacinsu Habibi Adamu game da gobarar a Yakasai.
Ya kuma yi nuni da cewa, nan take aka hada tawagar ceto daga ofishin hukumar kashe gobara da ke Sakatariyar Audu Bako a birnin Kano.
Jami’in hulda da jama’a ya yi nuni da cewa, ginin bene daya mai tsawon mita 40 da 30 da ake amfani da shi a matsayin gidan zama, daki daya da ke benen ne ya kone gaba daya sakamakon gobarar, yayin da falo daya ya kone kadan.
Ya ce, yaron ya makale a dakin da wutar ta kama har ta cinye shi. Kuma duk kokarin da aka yi na ceto shi kafin isowar ‘yan kwanakwana ya ci tura.
Saminu ya ci gaba da cewa, an ceto wanda abin ya shafa a sume kuma aka kai shi asibitin kwararru na Murtala Muhammed, inda likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa.
Ya ce, gobarar ta tashi ne sakamakon yadda yaron da abin ya shafa ke wasa da ashana a cikin daki.
Saminu ya bukaci iyaye da su daina jefa ’ya’yansu cikin hadari ta hanyar barin su ba tare da kula da su ba da kuma nisanta su da abubuwa masu hatsari.