Wata gobara ta ƙone motoci takwas ƙurmus da rumfunan katako takwas da kuma kayan aikin kafinta a layin Lawan Dambazau daura da digar jirgin kasa da ke Unguwar Gandu a Jihar Kano.
Lamarin ya faru a jiya Talata ya auku ne a wani kango da ake aikin kafinta da gyaran mota.
- Ramadan: Naira Biliyan 1.5 muka fitar kuɗin ciyarwa a Kano — Abba
- HOTUNA: Yadda Peter Obi ya yi buda baki da Musulmai a Kano
A cewar jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif Abudullahi, jami’an hukumar sun isa wurin ne bayan samun kiran gaggawa daga Ofishin ’yan sanda na Kwalli.
Ya ce, “Gobara ta ƙone rumfuna takwas ɗauke da kayan aikin kafinta da motoci takwas ƙurmus.
“Da taimakon Allah jami’anmu suka samu nasarar kashe gobarar kafin ta laso was rumfuna kusan 10 tare da Masallacin wucin gadi da kuma motoci 37 da aka ajiye a garejin.
Ya ƙara da cewa an yi amfani da motocin kashe gobara 5 da suka kawo ɗauki reshensu na Sakatariyar Audu Bako da ofishin kwana-kwana da ke Sharaɗa.
Ya ƙara da cewa, tartsatsin wutar lantarki daga masu aikin kafinta ne musabbabin tashin gobarar.