✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gini ya yi ajalin wata mata ya raunata ’ya’yanta a Kano

Mun yi ƙoƙarin fito da matar da ’ya’yanta daga cikin baraguzan ginin a raye.

Wani gini mai hawa ɗaya da ya rufta ya yi ajalin wata mata mai shekaru 35, Balaraba Tijjani a unguwar Makwarari da ke Jihar Kano.

Aminiya ta ruwaito cewa ginin ya faɗi ne sakamakon mamakon ruwa da aka kwana ana yi tun daren ranar Alhamis zuwa wayewar gari Juma’a.

A cewar mijin marigayiyar, Tijjani Magaji, ruftawar ginin ya kuma raunata ’ya’yansu biyu Abdulnasir ɗan shekara 11 da Abdallah dan shekara 13 waɗanda a yanzu haka suna kwance a asibiti.

Kakakin Hukumar Kwana-Kwana na Jihar Kano, Saminu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin.

Abdullahi ya bayyana cewa jami’ansu sun yi ƙoƙarin fito da matar da ’ya’yanta daga cikin baraguzan ginin a raye, inda suka garzaya da su Asibitin Ƙwararru na Murtala Mohammed.

Sai dai ya ce daga baya sun samu labarin rasuwar mahaifiyar yaran a yayin da take jinya a asibiti.