A ranar Lahadin makon jiya ne Gidauniyar Sa Ahmadu Bello, ta kai ziyara ga iyalan marigayi Alhaji Yusuf Maitama Sule Danmasamin Kano inda ta ba su kyautar Naira miliyan daya.
A jawabin jagoran ayairn Mai shari’a Mamman Nasir ya ce gidauniyar ta kai wa iyalan marigayin tallafi ne ba don kasancewarsa daya daga cikin wadanda suka kafa gidauniyar ba, illa saboda la’akari da irin gudunmawa da sadaukar da kai da ya yi wajen ginawa da ganin Najeriya ta ci gaba.
Mai shari’a Mamman Nasir wanda shi ne Galadiman Katsina kuma Hakimin Malumfashi ya ce kowa yana sane da gudunmawar da Danmasani ya bayar wajen hadin kan kasar nan, inda tsawon rayuwarsa duk inda ya bayar da lacca a taro, sai ya ja hankalin jama’a game da muhimmancin samun hadin kai tsakanin kabilun kasar nan.
Alhaji Mamman Nasir ya ce, “Muna godiya ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano bisa yadda suka yi hidimar karbar jama’a a jihar tare da yadda gwamnatin ta sanya sunan marigayin a jami’a sukutum. Mun gode kwarai da wannan karamci.”
Shugaban Kwamitin Amintatatu na Gidauniyar Alhaji Mu’azu Babangida Aliyu ya bayyana marigayi Danmasani da mutumin da ya samu babban rabo a wurin Allah, duba da yadda dimbin jama’a suka taru a wajen jana’izarsa. “A addininmu mun yarda cewa duk inda aka ga yawan jama’a wajen jana’izar mamaci to alama ce da take nuna cewa Allah Ya karbi ayyukan wannan mamaci, don haka muna yi wa marigayi Danmasani wannan zato cewa Allah Ya karbi ibadunsa da addu’o’insa. Muna kara nema masa afuwa a wajen Allah. Allah Ya sa Aljanar Firdausi ta zama makoma a gare shi,” inji tsohon Gwamna na Jihar Neja. “Kullum idan muka ce Arewa muna nufin Najeriya gaba daya, lura da yawan jama’a da fadin kasa idan har aka samu zaman lafiya da hadin kai a Arewa to za a samu zaman lafiya a sauran sasaan kasar nan,” inji shi.
Da yake mayar da jawabi a madadin iyalan marigayin, babban dansa Alhaji Mukhtari Yusuf Miatama Sule ya nuna godiyarsu game da karamcin da gidauniyar ta nuna musu, inda ya yi fatan dorewar alaka a tsakanin iyalan da gidauniyar.