✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidauniyar ADSI ta tallafa wa majinyata a Zamfara da Binuwe

Gidauniyar ADSI (Arewa Debelopment Support Initiatibe), mai rajin tallafawa ta fuskar ci gaban yankin Arewacin kasar nan, ta ce ta kai dauki ga daruruwan marasa…

Gidauniyar ADSI (Arewa Debelopment Support Initiatibe), mai rajin tallafawa ta fuskar ci gaban yankin Arewacin kasar nan, ta ce ta kai dauki ga daruruwan marasa lafiya a Jihohin Binuwe da kuma Zamfara, a makonni biyun farko da fara gudanar da aikace-aikacenta a yankin.

Bayanin hakan na ya fito ne daga bakin wadda ta assasa gidauniyar, Hajiya Khuraira Musa, a yayin wani taron manema labarai da gidauniyar ta kira, a Abuja, a farkon makon nan.

Ta ce gidauniyar ta fara da Jihohin Zamfara da Kebbi a matsayin zakaran gwajin dafi, kuma sun ziyarci asibitoci a yankunan kananan hukumomi biyar a Jihar Zamfara inda suka duba marasa lafiya 150 a gadajen asibiti tare da tallafa musu. Yayin da a Jihar Binuwe ma gidauniyar ta tallafawa dimbin majinyata ta hanyar biya musu kudin asibiti da ba su kudin sayen magani.

Ta kara da cewa, nan gaba gidauniyar za ta kaddamar da ayyukanta a jihar Kaduna, inda a wannan karon za ta karkata akalar tallafin da take bayarwa zuwa bangaren ‘koyar da sana’o’i’ musamman ga matasa.

A cewar ta shirye-shirye sun kankama ta fuskar hakan, kuma daga nan gidauniyar za ta wuce zuwa Jihar Filato kafin ta karade sauran jihohin arewacin Najeriya.

“Ba za mu ci gaba da zura wa gwamnati ido don ta samar mana da komai ita kadai ba. Lallai ne mu hada karfi da karfe wajen lalubo hanyoyin da za mu dafawa gwamnatin don ganin an inganta rayuwar marasa galihun cikinmu tare da kawo ci gaba mai ma’ana a yankin na arewa.” Inji Hajiya Khuraira.

Hajiya Khuraira ta ce babban makasudin kafa gidauniyar ita ce, hada hancin kwarewar ilmi da kuma na tattalin arzikin jama’ar arewa da zimmar kawar da barazana tare da kawo ci gaba a yankin, hakan mai yiwuwa ne sakamakon yadda suke da alaka da mutane daban- daban.

Da take bayani game da yadda gidauniyar ke samun kudin shiga don aiwatar da aikace-aikacenta, cewa ta yi an dora wa dukkan membobin gidauniyar bayar da gudummawa na akalla Naira dubu biyu kowane wata, sannan tana samun gudummawa daga daidaikun jama’a.