✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gidan rediyon Kwankwaso ya fara aiki a Kano

Gidan rediyon Nasara FM mallakin tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso ya fara aiki

Sabon gidan rediyon Nasara FM wanda tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso ya kafa a jihar ya fara gwaji.

An kaddamar da gidan rediyon mai taken “Amanar Talaka” wanda za a a mita 98.5 zangon fm ne a ranar Alhamis 22 ga watan Oktoba.

Da yake jawabi yayin bikin bude gidan rediyon Kwankwaso ya bayyana  kafafen yada labarai a matsayin wurin wayar da kan al’uma da tafarkin dimokuradiyya baya ga rawar da suke takawa ta kowane fanni.

“Dukkanmu mun gamsu cewa bayan ilimantar da al’umma babu wani abu mai muhimmanci kamar wayar da kan al’uma ta hanyar kafafen yada labarai, saboda irin muhimmancin da fannin ke da shi wurin wayar da kan al’umma da ilimantar da su”.

Ya ci gaba da cewa, “wannan rediyon mun yi masa take da Amanar Talaka saboda ya wayar da kan talaka, ya samar da sana’o’i da ayyukan yi da saurarar koke-kokensu”.

“Ina mai sanar muku cewa ba ya daga cikin kudurinmu na bude wannan tashar rediyo ya zama don a fifita bukatunmu ko daga darajar siyasarmu, face ya zama muryar talaka ba bai wa wani mutum guda fifiko ba.

“Fatan Nasara rediyo shi ne hidimta wa jama’a da inganta aikin jarida”.