✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gibin kudin shiga ke gurgunta wutar lantarki a Najeriya —APGC

Kungiyar Masu Kamfanonin Samar da Wutar Lantarki ta kasa (APGC) ta ce har yanzu suna bin bashin kudin aikin Naira Tiriliyan 1.64 na tsawon shekara…

Kungiyar Masu Kamfanonin Samar da Wutar Lantarki ta kasa (APGC) ta ce har yanzu suna bin bashin kudin aikin Naira Tiriliyan 1.64 na tsawon shekara bakwai a Najeriya.

Babbar Sakatariyar kungiyar, Dokta Joy Ogaji, ta ce kudin makamashi ma da  Hukumar kula da hada-hadar wutar lantarki (NBET) ya kamata ta biya kamfanonin (Gencos) kowanne wata, ana samun gibi.

Hakan a cewarta, ya sanya an samu karancin kudaden shiga a GenCos din, har ba sa iya sayen wadatacciyar iskar gas da sauran abubuwan da za su yi amfani da su wajen inganta samar da wutar lantarki a Najeriya.

Domin magance wannan matsala dai  Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) a ranar 1 ga Yuli, 2022, ta samar da sabon tsarin kasuwancin wutar karkashin yarjejeniyar da za ta tabbatar da akalla an samar da megawatt 5,300 na wutar a kullum, tare da sanya takunkumi ga wadanda za su yi aikin.

To sai dai Wani jami’i a NERC ya ce masu gudanar da harkar wutar a wannan watan na da kwarin gwiwar cewa wutar za ta kara inganta, kasancewar kamfanonin samar da ita za su kara karfinta saboda ruwan sama da ya karu.

Idan ba a manta ba, kafin lalacewar wutar ta kasa a watan Maris, APGC ta koka kan yawan bashin da suke bi, da kuma fargabar durkushewarsu.

Haka kuma bayanai da Aminiya ta samu na nuna cewa tun a watan Janairun 2022 da gwamnati ta dakatar da bada tallafin wutar lantarkin (PAF), kudaden shigar GenCos din ya koma kacokan kan DisCos.

Lamarin dai ya janyo kasuwarsu ta fadi zuwa kashi 50.8, har sai a watan Fabrairu ya karu zuwa kashi 59.82.

Sai dai a watan Maris an samu koma-baya, bayan ya sake raguwa zuwa kashi 48.35, kafin daga bisani ya haura zuwa kashi 60.62 a watan Afrilun 2022.

A hannu guda dai tun a watan Maris din 2022 ne Ministar Kudi Zainab Ahmed ta ce Gwamnatin Tarayya ta janye tallafin wutar lantarkin da kadan da kadan, ta hanyar kara kudin wutar lokaci zuwa lokaci.

Da yake tsokaci game da biyan kamfanonin samar da wutar lantarkin, Babban Daraktan kungiyar masu rarraba wutar lantarki ta Najeriya (ANED), Sunday Oduntan, ya bayyana cewa har sai gwamnati ta aiwatar da alkawarinta na yarjejeniyar sannan matsalolin da ake samu a fannin za su kau.

Oduntan ya shaida wa Aminiya cewa, duk da sake fasalin kamfanonin rarraba hasken wutar lantarkin, ba za a samu wani gagarumin ci gaba ba, har sai dai gwamnati ta samar da jadawalin farashin wutar daidai da gudanar ita, da kuma daina tsoma baki, ko aiwatar da duk wasu garambawul na kasuwanci a bangaren ba tare da shawartar su ba.