✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gerrard Pique ya yi ritaya daga kwallon kafa

Dan wasan ya buga wasanni 573 sannan ya zura kwallo 57 a raga.

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Gerrard Pique, ya ce wasan da kungiyarsa za ta yi da Almeria a ranar Asabar shi ne wasansa na karshe a filin wasa na Camp Nou.

Dan wasan ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis.

Ya shaida cewar wasan da Barcelona za ta yi a ranar Asabar shi ne na karshe dai zai yi da kungiyar a gida, kafin a fara Gasar Kofin Duniya.

Bayan yanke hukuncin dan wasan, Barcelona za ta warware kwantaragin da ta kulla da shi wanda zai kare a karshen kakar wasanni ta bana.

Pique ya buga wasanni 573, sannan ya zura kwallo 57 a raga a rayuwarsa ta kwallon kafa.

Dan wasan ya kuma lashe kofi 36 a matsayin dan wasan bayan Barcelona.