A kokarin ta na rage wa ’yan gudun hijira da marasa gata kuncin rayuwa a Jihar Yobe, Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar (YOSEMA), ta raba buhunan shinkafa 1,200 a kowacce daga kananan hukumomi 17 da ke jihar.
Da yake jawabi kan yadda rabon kayan Babban Sakataren Hukumar, Muhammad Goje, ya ce al’ummar garin Geidam za a hada musu da kayayyakin da bana abinci ba a cikin nasu kason.
An cafke shugaban ’yan bindigar Neja
Kwastam sun kashe mutum 5 a garin kama shinkafa
Janar Dogonyaro: Buhari na alhinin mutuwar sojan da ya yi jawabin yi masa juyin mulki
’Yan bindiga sun yi wa matar aure fyaden gandu
Goje, ya ce Hukumar na raba kayan ne da hadin gwiwar shugabannin kananan hukumomi da zimmar ba da tallafin kayan abinci ga marasa galihu bisa umarnin Gwamna Mai Mala Buni.
“Kayan abincin an bayar ne da su da zimmar tallafa wa dattawa da mata, magidanta, nakasassu da talakawa a mazabu 178 da ake da su a jihar”.
Da yake karbar takardar rabon kayan a madadin kananan hukumomin shugaban shugabannin kananan hukumomin jihar, Bukar Adamu, ya tabbatar da cewa za su raba kayan ga mutanen da aka kawo domin su.