✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gbajabiamila ya yi murabus daga Majalisar Wakilai

A baya-bayan nan shugaba Tinubu ya nada Gbajabiamila shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin tarayya.

Tsohon shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila, ya sauka daga kujerarsa.

Mr. Gbajabiamala ya sauka daga wakilcin mazaɓar Surulere 1, da ke Legas saboda kama aiki a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa.

Da safiyar Laraba ne Mr. Gbajabiamila ya miƙa takardar barin majalisar gaban sabon shugaban majalisar, Tajuddeen Abbas.

A tsawon shekaru 20 da Mr. Gbajabiamila ya yi a Majalisar ya riƙe muƙaman shugaban marasa rinjaye, shugaban masu rinjaye, da shugaban majalisar.