Mazauna garin Jalingo a Jihar Taraba sun koka kan yadda farashin gawayi da icen girki suka yi tashin gwauron zabo.
A halin yanzu farashin dauri daya na icen girki ya tashi zuwa N500, daga N200 da ake sayar da shi a makonnin baya.
- Buhari ya dukufa wajen fitar da ’yan Najeriya daga talauci —Sadiya
- Sojoji sun dakile sabon harin Boko Haram a Damboa
Buhun gawayi kuma ya tashi daga N900 ya koma Naira 2,300 saboda karancinsa da kuam rashin icen girki a garin na Jalingo.
Aminiya ta gano farashin ya yi tashin gwauron zabon ne saboda matsalar tsaro da ke hana masu sana’ar shiga dazuka kafin su samar da su.
Bugu da kari an samu karuwa a yadda mutane ke yin tururuwar amfani da su a wurare daban-daban.
Wani mai sayar da ice, Malam Yakubu Sani karuwar bukatar gawayi da ice a tsakanin mazauna garin ne saboda tsadar kananzir da gas din girki.
Malam Yakubu ya kara da cewa kudin motar daukar kayan ya karu, sannan yawancin masu sannan shiga daji domin yin ice na da matukar hadari saboda ayyukan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
“Yawancin masu sana’ar tamu sun fice daga cikin dazuwa saboda rashin tsaro, wanda hakan ya sa ake famda da karancinsu,” kamar yadda ya bayyana wa wakilinmu a zantawar da suka yi.
Zubairu Hudu, mai sayar da gawayi ya ce karuwar masu neman gawayi da icen girki da kuma karancinsa ne ya sa suka yi tashin gwauron zabo.