✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gawa ta yi shekara 1 ana tunanin suma ne

An mika wa dangin mutumin takardar shaidar mutuwarsa, amma suka ki yarda da ya rasu.

Iyalin wani mutum mai shekara 35 da ya mutu a watan Afrilun bara sakamakon cutar Coronavirus sun ci gaba da rayuwa da gawarsa tun daga lokacin, inda suke tunanin suma ya yi.

Vimlesh Sonkar, jami’in haraji a birnin Ahmedabad na Jihar Gijarat da ke Indiya da aka kwantar da shi a asibitin Moti a ranar 19 ga Afrilun 2021 kuma ya mutu bayan kwana uku sakamakon kamuwa da Coronavirus.

An mika wa dangin mutumin takardar shaidar mutuwarsa, amma suka ki yarda da ya rasu.

Maimakon haka sai suka kai gawarsa gida suka ci gaba da kula da shi, da tunanin zai farka.

An gano gawar mutumin ne kwanaki kadan da suka gabata, lokacin da aka tura wata tawaga daga wurin aikinsa domin gudanar da bincike kan rashin farkawarsa na tsawon lokaci.

Babban Jami’in Kula da Lafiya (CMO) na Kanpur, Alok Ranjan ya bayyana wa jaridar Sunday Express cewa, “Mutumin ya mutu ne a ranar 22 ga Afrilu, 2021 yayin da annobar Coronavirus ta sake barkewar a karo na biyu.

Ya kasance yana da ciwon huhu. “Bayan ya mutu, an kai shi gidan jinya na yankin, inda aka ce ya mutu.

“An kuma bayar da takardar shaidar mutuwarsa, inda aka bayyana cewa, ciwon hunhu ne ya yi sanadiyar rayuwarsa.”

Sai dai kuma ba a san dalilin da ya sa dangin Vimlesh ba su yarda da rahoton asibiti da ya nuna cewa ya mutu ba.

Jaridar Times of India ta ruwaito cewa, sun dauki gawarsa zuwa wani asibiti domin karin wani gwajin.

Ko da likitocin da ke wurin suka tabbatar da rasuwarsa, sun dauki gawar tasa sun koma gida suna yi mata magani kamar ta mai ciwon suma da zai iya tashi wata rana.

A cewar Mujallar Free Press, dangin sun yi shirin yi wa mutumin ibadarsa ta karshe, inda da farko suka sanya na’urar ‘oximeter’ a daya daga cikin yatsunsa don jin ko yana numfashi.

Bayan na’urar ta nuna bugun jini da kuma iskar numfashi ‘oxygen’ a cikin jininsa, sai suka yanke shawarar cewa har yanzu yana nan da rai suka soke jana’izar.

Iyalan Vimlesh Sonkar sun ajiye gawarsa a cikin gida har tsawon shekara guda da rabi, suna tunanin cewa dogon suma ya yi kuma wata rana zai farka.

Matarsa da iyayensa da ’yan uwansa da suke zaune a gida daya, sun ba shi kulawa, inda suka rika amfani da maganin kashe kwayoyin cuta na Dettol sau uku a rana.

Haka kuma, sun rika canza tufafinsa a kullum tare da kunna na’urar sanyaya daki a koyaushe.

Wani babban jami’in ‘yan sanda ya shaida wa jaridar Indian Express cewa, “Duk lokacin da ma’aikatan ofishinsa suka tambayi danginsa game da inda yake, sai su ce Vimlesh ba shi da lafiya.

“Iyalin kuma sun kawo silinda ta iskar numfashi suka gaya wa mutanen yankin cewa, ya yi dogon suma ne kuma ana yi masa magani a gida.

“ Sun tabbata cewa yana raye kuma zai samu sauki.”