✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gasar Zakarun Turai: Wasannin da za a fafata ranar Laraba

Z­a a buga wasannin ne da misalin karfe 7:45 na yamma, da kuma karfe 8:00 na dare.

Za a ci gaba da wasa na uku-uku a cikin rukuni a gasar Zakarun Turai wato Champions League ranar Laraba, inda za a yi karawa takwas.

Z­a a buga wasannin ne da misalin karfe 7:45 na yamma, da kuma karfe 8:00 na dare.

Ga rukunan da kungiyoyin da za su fafata a daren, bayan hutun makonni biyu da aka je:

Rukunin E

  • Chelsea vs AC Milan
  • Red Bull Salzburg vs Dinamo Zagreb

Rukunin F

  • RB Leipzig vs Celtic
  • Real Madrid vs Shakhtar Donetsk

Rukunin G

  • Manchester City vs FC Copenhagen
  • Sevilla vs Borussia Dortmun

Rukunin H

  • Benfica vs Paris Saint-Germain
  • Juventus vs Maccabi Haifa

Ana dai ganin cewa, wasan da zai fi zafi a rukuni na biyar shi ne fafatawar da za a yi tsakanin Chelsea da AC Milan.

A rukuni na shida kuwa, wasan da zai fi daukar hankali shi ne wanda za a gwabza tsakanin Real Madrid mai rike da kofin da Shahktar Donetsk da .

Wasan da  za a kai ruwa rana tsakanin Sevilla da Borussia Dortmund shi ne zai fi daukar hankali a rukuni na bakwai.