✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Olamfik: Babu dan Najeriya a cikin masu yin alkalanci

A ranatar Litinin da ta wuce ne Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta fitar da jerin sunayen wadanda za su yi alkalanci a…

 Shugaban Hukumar FIFA Gianni InfantinoA ranatar Litinin da ta wuce ne Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta fitar da jerin sunayen wadanda za su yi alkalanci a bangaren wasan kwallon kafa a gasar wasannin Olamfik da zai gudana a Brazil a bana.
Sai dai daga cikin jerin sunayen alkalan da hukumar ta fitar, babu wani alkalin wasa da ta gayyato daga Najeriya.
Kwamitin da ke kula da zakulo alkalan wasa daga sassan duniya sun tabbatar da zabo alkalan wasa 88 ne daga cikin kasashe 40 na duniya amma babu dan Najeriya a ciki.
Kamar yadda rahoton ya nuna, kimanin alkalan wasa 18 ne ake sa ran za su yi alkalanci a bangaren kwallon kafa na maza tare da masu taimaka musu su kimanin 32.  A bangaren mata kuwa an zabo alkalan wasa su kimanin 14 ne tare da masu taimaka musu su kimanin 24.
Kwamitin ya zabo alkalan wasa hudu ne daga Nahiyar Afirka da suka hada da Kimbira Bernadettar daga Malawi da Camara Dhibril daga Senegal da Samba El Hadji Malikck daga Senegal da kuma Ahmed Waheed daga Sudan.
Za a fara wasan kwallon kafa a bangaren maza ne a gasar ta Olamfik daga ranakun 3 zuwa 21 ga watan Agustan wannan shekara yayin da ake sa ran wasan karshe zai gudana ne a filin wasa na Marcana da ke Brazil.
Za a yi amfani da filayen wasannin kwallon kafa bakwai ne wajen gudanar da gasar ciki har da filin wasan da aka yi amfani da shi wajen yin gasar cin kofin duniya a 2014.
Sauran filayen wasannin da za a yi amfani da su sun hada da na Belo Horrizonte da na Brasillia da na Mannus da na Rio de Janeiro da na Salbador da kuma na Sao Paulo.
Wannan ya nuna har yanzu alkalan wasan da ke Najeriya ba su samu gogewar da ta dace  ba  ganin an zabi alkalin wasa daga Sudan a gasar Olamfik amma babu dan Najeriya.