✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Neman Gurbin Cin Kofin Afirka: Najeriya ta yi kunnen doki da Afirka ta Kudu *Kamaru ta yi wasan kura da Kwaddebuwa

A shekaranjiya Laraba ne kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles ta fafata da kasar Afirka ta Kudu a cigaba da gasar neman gurbin…

A shekaranjiya Laraba ne kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles ta fafata da kasar Afirka ta Kudu a cigaba da gasar neman gurbin zuwa  cin kofin Afirka da zai gudana a shekarar 2016.
Najeriya ta yi wasanta ne da kasar Afirka ta Kudu a Cape Town inda aka tashi 0-0.  Sai dai Afirka ta Kudu ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta samu nasara a wasan amma hakarta ba ta cimma ruwa ba.
A halin yanzu Afirka ta Kudu ta hada maki hudu kenan a wasanni biyu da ta yi.  A wasanta na farko ta lallasa Sudan ne da ci 3-0.
A bangaren Najeriya kuwa, yanzu ta hada maki daya ne kacal daga wasanni biyu.  A wasanta na farko a gida ta samu rashin nasara ne a wajen Kongo bayan ta lallasa ta da ci 3-2 a garin Kalaba sai kuma ga shi ta yi kunnen doki da Afirka ta Kudu  da hakan ya sa Najeriya take a matsayi na uku da maki 1.
A daya bangaren wasa a tsakanin Kongo da Sudan kuwa, Kongo ce ta lallasa Sudan da ci 2-0.  Don haka yanzu Kongo ce take kan gaba a rukunin da Najeriya take fafatawa da maki 6 daga wasanni biyu, sai Afirka ta Kudu ta biyu da maki hudu sai Najeriya mai maki 1 yayin da Sudan take ta kashin baya babu maki ko daya.  kasashen da suka kasance na daya da na biyu a kowane rukuni ne za su halarci gasar cin kofin Afirka idan an kammala dukkan wasannin.
A wasan da aka yi tsakanin kasashen Kamaru da na Kwaddebuwa kuwa, Kamaru ce ta yi wasan kura da Kwaddebuwa inda ta zurara mata kwallaye hudu da daya.
Sauran sakamakon wasanni su ne: Malawi 3-2 Habasha, Angola 0-3 Burkina Faso, Lesotho 1-1 Gabon, Sierra Leone 0-2 Dr Congo,Togo 2-3 Ghana, Uganda 2-0 Guinea, Mozambikue 1-1 Nijar, Cape berde 2-1 Zambia.  Sauran wasannin su ne Botswana 0-2 Senegal sai Egypt 0-1 Tunisiya.