✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar neman gurbi a cin kofin Afirka: Najeriya ta farfado

A shekaranjiya Laraba ne kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles ta lallasa ta Sudan a cigaba da gasar neman gurbi na cin kofin…

A shekaranjiya Laraba ne kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles ta lallasa ta Sudan a cigaba da gasar neman gurbi na cin kofin Afirka da zai gudana a kasar Maroko a shekara mai zuwa.

Kafin wasan, Najeriya Super Eagles tana cikin tsaka mai wuya ne bayan ta hada maki daya kacal daga wasanni uku da ta yi. A wasanta na farko da kasar Kongo, ta sha kashi ne a gida da ci 1-0 a garin Kalaba, yayin da a wasa na biyu kuma ta yi kunnen doki da Afirka ta Kudu a filin wasansu yayin da a wasa na uku kuma da aka buga a ranar Asabar da ta wuce a Sudan, Sudan ce ta lallasa Najeriya da ci daya mai ban haushi.
Don haka wasan shekaranjiya ya yi zafi don dukkan kasashen biyu suna neman nasara ne don ganin sun farfado a gasar.
A daidai minti na 48 ne shahararren dan kwallon Najeriya da ke wasa a kulob din CSKA Mosko na Rasha watau Ahmed Musa ya jefa wa Najeriya kwallonta na farko a raga amma a minti na 58 sai dan kwallon Sudan mai suna Mohammed Abdullahi ya farke cin da ake yi musu. Nan fa filin wasa na Abuja ya yi tsit, inda murna ta koma ciki saboda bakin ciki. A daidai minti na 66 ne dan kwallon Najeriya mai suna Aaron Samuel Dianare ya sake jafe wa Najeriya kwallonta na biyu a raga inda filin wasa ya rude da tafi da murna. Hatta shi kansa mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Stephen Keshi, ba a bar shi a baya ba wajen nuna farin cikinsa a fili.
Haka aka cigaba da fafatawa sai a minti na 87 watau minti uku kacal kafin a kare wasan dan kwallon Najeriya Ahmed Musa ya sake jefa kwallonsa ta biyu a raga da hakan ya sa wasa ya koma 3-1.
Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta kasa sun mamaye filin wasan saboda farin ciki jim kadan bayan an tashi wasan. Da ya daga cikinsu sun yaba da irin namijin kokatin da ’yan kwallon Najeriya suka nuna a wasan. Wasu daga cikin sun bayyana cewa da tun farko haka kungiyar take wasa, da ba ta fada cikin mayuwacin halin da ta tsinci kanta a gasar ba.
Yanzu dai Najeriya ta koma ta uku a rukunin bayan ta hada maki 4 daga wasannin 4. Ita kuma Sudan ta koma ta karshe da maki uku daga wasanni hudu.