✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar La-Liga: Gobe Barbelona za ta shawo ta da Sebilla

A gasar  rukuni-rukuni na Sifen da aka fi sani da La-Liga, a gobe Asabar za a shawo ta a tsakanin kulob din FB Barbelona da…

A gasar  rukuni-rukuni na Sifen da aka fi sani da La-Liga, a gobe Asabar za a shawo ta a tsakanin kulob din FB Barbelona da na Sebilla.

Wasan zai yi zafi, ganin za a hadu ne da qungiyar da ke saman tebur a gasar wato Sebilla da kuma ta Barbelona da take matsayi na 2.

Duk qungiyar da ta sake aka doke ta a wasan, sai buzunta ganin qungiyoyin da ke biye a saman teburin gasar suna rububi ne wajen ganin sun karbi ragamar teburin, idan suka samu damar yin haka.

Shi ma wasa ne da aka sa ran gidajen kallon qwallon qafa za su bika maqil da masoya qwallon qafa don kashe qwarqwatar ido.

Tuni magoya bayan qungiyoyin biyu suka shiga babar baki game da qungiyar da suke ganin ita za ta samu nasara a wasan.