Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta bukaci dukkanin tawagogin kasashe 32 da za su fafata a Gasar Kofin Duniya, da su mayar da hankali kan abin da ya kai su Qatar, wanda shi ne kwallon kafa.
FIFA ta bukaci dukkanin tawagogin kasashen da su mutunta duk al’adun kasar Qatar wadda za ta yi wa Babbar Gasar masaukin baki.
- Tinubu ba shi da lokacin zuwa tarukan muhawara –APC
- Sauyin Kudi: Canjin Fam ya kai N1,000 a wurin ’yan canji
Kiran na FIFA ya zo ne a daidai lokacin da ce-ce-ku-ce ya mamaye gasar da za a fara a ranar 20 ga watan Nuwamban da muke ciki.
Bayanai sun ce ana ci gaba da ce-ce-ku-cen musamman game da cin zarafin dan Adam da ake zargin kasar da aikatawa baya ga matakinta na haramta badala.
Kasashen Turai da dama gami da wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam na caccakar Qatar kan matsayinta na adawa da auren jinsi daya.
Haka kuma, ana gunaguni kan yadda ake zargin kasar da take hakkin dan Adam, musamman akan mu’amala da ma’aikata bakin haure.
Rahotanni na cewa, akwai ’yan wasan ma da suka shirya gudanar da zanga-zangar lumana yayin da aka fara gasar ta Cin Kofin Duniya.
’Yan wasan za su yi zanga-zangar ce don kalubalantar salon gwamnatin Qatar na tauye hakkin dan Adam a Paris, da sauran garuruwan Faransa.
Kazalika, ’yan wasan sun ce ba za su nuna wasannin gasar cin kofin duniya a wuraren da jama’a ke taruwa a filaye ba, duk da cewa Faransa ce ke rike da kofin a yanzu.