A Jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu za a yi ta ta kare a gasar rukuni-rukuni a Ingila da aka fi sani da Firimiya. Kawo yanzu an yi wasanni 37 saura wasa daya ke nan a kammala. Sai dai a jibi wasanni biyu ne za su fi daukar hankali wato wasa a tsakanin Brighton da Manchester City da kuma wasa a tsakanin Liberpool da Wolberhampton.
Ya zuwa yau, kulob din Manchester City ne yake saman teburin gasar da maki 95 yayin da Liberpool ke biye da maki 94.
Komai zai iya faruwa, idan Man City ta yi kunnen doki ko ta yi sakaci aka doke ta, sannan Liberpool ta samu nasara ko shakka babu Liberpool ce za ta zama zakara.
Amma idan Man City ta samu nasara babu tantama ita ce za ta sake lashe kofin a karo na biyu a jere.
Idan za a tuna Liberpool ba ta taba lashe wannan kofi ba tun bayan da aka canja masa suna zuwa gasar Firimiya a shekarar 2000 kimanin shekara 19 da suka gabata.
Don haka masana harkar kwallo suke ganin kallo ya koma sama, kan yadda wasan zai kaya a tsakanin ta daya Man City da kuma ta biyu Liberpool.
Kamar yadda jadawalin gasar ya nuna, za a yi wasanni 10 ne duk a rana daya kuma a lokaci daya. Abin da Hausawa ke cewa “kowa tasa ta fisshe shi.”
Kungiyoyi uku da suka samu koma baya su ne Cardiff City da Fulham da kuma Huddesfield Town, yayin da kungiyoyi hudun da suke saman teburin gasar ce za su halarci gasar Zakarun Turai a kaka mai zuwa. Na biyar da na shida kuma za su halarci gasar Kofin Turai na Europa.
Masoya kwallon kafa sun zuba ido su ga yadda wasannin za su kaya a jibi da misalin karfe 3 na rana agogon Najeriya