A gobe Asabar idan Allah Ya kai mu za a yi wasa mai zafi a gasar Firimiya ta Ingila a tsakanin kulob din Chelsea da Manchester City.
Wasan zai gudana ne a filin wasa na Chelsea da ake kira Stamford Bridge da misalin karfe 6:30 na yamma agogon Najeriya.
Kawo yanzu kulob din Manchester City ne yake saman teburin gasar da maki 41 a wasanni 15 yayin da kulob din Chelsea yake matsayi na 4 a wasanni 15 da maki 31.
Tun bayan da aka fara gasar ta bana kulob din Man City bai samu rashin nasara ba, yayin da kulob din Chelsea ya samu rashin nasara sau biyu.
Idan Chelsea ta samu nasara a wasan, to za ta karya wa Man City lago a matsayin ta farko da ta fara doke City a gasar ta bana. Amma idan City ta samu nasara, to za ta ci gaba da jan ragamar gasar kuma zai kasance ita ce kulob na uku da ta doke Chelsea a gasar ta bana.
Kulob din Chelsea dai yana takama da zaratan ’yan kwallo irin su Eden Hazard da Willian da Pedro da sauransu, yayin da Man City ke da zaratan ’yan kwallo irin su Raheem Sterling da Sergio Aguerro da Fernandinho da sauransu.
Wasa ne da ake sa ran gidajen kallon kwallo musamman a Arewacin Najeriya za su cika don kashe kwarkwatar ido.