A jibi Lahadi 2 ga watan Fabairu ne ake sa ran kungiyoyin kwallon kafa na Ghana da na Libya za su fafata a wasan karshe a gasar cin kofin Afirka na ’yan gida karo na hudu.
Tun da farko Libya ta samu nasara a wasanta da kasar Mozambik ne a wasan farko da aka fara da misalin karfe hudu agogon Najeriya. Kodayake a bugun daga kai sai mai tsaron gida (fanariti) wasan ya kaya bayan da Mozamboik ta barar da kwallaye hudu yayin da Libya kuma ta barar da uku.
Bayan an kammala wasansu da misalin karfe bakwai da rabi agogon Najeriya aka fara wasan Super Eagles da Ghana.
Shi ma sai da aka kwashe mintuna 120 ana ba ta kashi wasan bai kaya ba sai a bugun daga kai sai mai tsaron gida (fanariti).
Abin mamaki shi ne yadda ’yan kwallon Super Eagles suka kasa zura kwallo a ragar Ghana duk da katin korar da dan kwallonsu ya samu a wajen minti 77 da fara wasa.
Najeriya ta yi ta kai kora amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba da hakan ta sa aka kara lokaci na minti talatin watau (edtra time).
Duk da karin Najeriya ba ta samu galaba a kan Ghana ba kuma wasan bai kaya ba sai da aka kai matakin bugun daga kai sai mai tsaron gida.
A fanaritin ne Najeriya ta barar da kwallaye biyu yayin da ta jefa daya a raga yayin da Ghana ta zura kwallayenta uku a ba tare da barar da ko daya ba da hakan ya sa ta kai matakin karshe.
Yanzu dai kallo ya koma sama tun da Ghana ce da Libya za su yi wasan karshe.
Tuni kasar Libya ta barke da sowa ganin wannan shi ne karon farko da kasar za ta buga wasan karshe a wannan gasa duk da irin matsalolin siyasar da take fama da shi.
Haka su ma kasar Ghana, jim kadan da tashi wasan ne suka shiga murnar nasarar da suka samu a kan Najeriya a wasan, inda suka yi fatar lashe kofin idan suka hadu da Libya a jibi.
Najeriya za ta hadu a neman matsayi na uku ne a tsakaninta da Mozambik a gobe Asabar
Gasar Cin Kofin Afirka: Jibi Ghana za ta kara da Libya a wasan karshe
A jibi Lahadi 2 ga watan Fabairu ne ake sa ran kungiyoyin kwallon kafa na Ghana da na Libya za su fafata a wasan karshe…
