✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Cin Kofin Afirka: Gobe Najeriya za ta hadu da Maroko

A Gobe Asabar idan Allah Ya kaimu kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta kasa za ta hadu da kasar Maroko a wasan kusa da…

'Yan kwallon Super Eagles suna murnar jefa kwallo a ragaA Gobe Asabar idan Allah Ya kaimu kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta kasa za ta hadu da kasar Maroko a wasan kusa da na karshe (Kwata-Fainal) a gasar cin kofin Nahiyar Afirka na ’yan gida da ake wa lakabi da CHAN  da yanzu haka yake gudana a kasar Afirka ta Kudu.
Maroko dai ta samu kaiwa wannan mataki  ne bayan ta lallasa kasar Uganda da ci 3 da 1 yayin da Najeriya kuma ta haye wannan mataki bayan ta lallasa mai masaukin baki Afirka ta Kudu da ci 3 babu ko daya.
 kasashen biyu za su yi kokarin ganin sun samu a kokarin kai wa matakin kusa da na karshe watau Semi-Fainal.
Wannan shi ne karo na uku da gasar ke gudana amma Najeriya ba ta taba lashe kofin ba.
Idan za a iya tunawa, Najeriya ce ta lashe kofin Afirka a bara wanda shi ma ya gudana a Afirka ta Kudu.