’Yan Najeriya na kara fuskantar karancin gas din girki, yayin da farashinsa ke ci gaba da tashin gwauron zabo a fadin kasar nan, kamar yadda binciken Aminiya ya nuna.
Rahotanni sun suna tsadar gas din na girki ta fi kamari a garuruwan Legas, Kano, Maiduguri da dai sauransu.
- Hisbah ta kori jami’inta kan hada kai da masu ayyukan badala
- Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 79 cikin wata 10 a Gombe – FRSC
Dillalan gas din girki sun bayyana cewa karancin nasa na dan lokaci ne, kuma hakan ya faru ne sakamakon matsala da jiragen da ke jigilarsa suka samu wajen kawo shi tashoshin riragen ruwa da ke Legas.
Yanzu haka, da dama daga cikin wuraren sayar da gas din giriki ba sa aiki saboda rashinsa wanda za su sayar.
A Legas ma babu
Bincikenmu a gidajen mai da shagunan sayar da gas din girki a sassan jihar Legas ya gano cewa kadan ne daga cikinsu ke sayar da shi, a farashi daban-daban.
A Iyana Ipaja, wakilinmu ya ziyarci gidajen mai guda biyu inda daya ne kawai ke sayar da gas din.
A gidan mai na Petrocam da ke Ile-Epo, Oke Odo, ana ci gaba da sayar da tukunyar gas mai nauyin kilogiram 12.5 kan Naira 12,000 a jiya (Talata).
Daya daga cikin ma’aikatan ya shaida wa wakilinmu cewa har yanzu gidan man na jiran a kawo musu gas din girki duk da cewa mutane na tururuwar zuwa sayen gas din.
Kilo N1,300 a Kano
Wakilinmu ya ruwaito cewa a Kano ana fama da karancin gas din duk da cewa ana sayar da kilo a kan Naira 1,300 a wasu wuraren.
Wani dillalin sayar da gas din girki mai suna Abubakar Aliyu, ya ce, “Gas din girki ba shi da yawa a kasa duk da cewa duk lokacin da na je sayowa da kyar nake samowa domin a wasu lokuta nakan saya kai-tsaye daga kamfani, wasu lokuta idan muka je sai su sanar da mu cewar ana fama da karancinsa.”
A nasa bangaren Adamu Abdullahi wanda shi ma dillali ne ya ce, “Gaskiya muna fama da karancin gas idan aka kwatanta da kwanakin baya.
“Yanzu idan muka je kamfani yakan dauki tsawon lokaci kafin mu shiga ciki, domin mutum na shafe tsawon lokaci tun daga safe har zuwa yamma bai samu ba.”
Manajan kamfanin mai na Bilkaka Oil & Gas, Auwal Umar Baba ya ce: “Gaskiya akwai karancin gas duba da cewa ko a Legas da muke sayo shi ma ba ya samuwa. Wannan na iya zama matsala ga kasuwancin gas.”
Farashi ya bambanta a Maiduguri
A Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ana fama da karancin gas din girki
Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa farashin gas ya yi tashin gwauron zabi ne sakamakon karancin sa da ake fama da shi a jihar.
Muhammad Abacha Maidoki, wani ma’aikacin kamfanin mai na Machar Oil and Gas Limited, ya dora laifin karin farashin gas din a kan rashin samun kudin da ake bukata da kuma sufuri.
“A yanzu direbobinmu sun shafe makonni biyu a kan hanya domin samun gas maimakon kwanaki biyar da suka saba yi a baya saboda rashin hanyoyin mota.”
Manajan wani gidan mai da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa yanzu haka ana sayar da kilogiram daya na gas akan Naira 1,166 a wurinsa.
A duk wuraren sayar da gas da aka ziyarta, farashin ya bambanta. Yayin da wasu ke karbar N14,000 kan kowace tunkuyar gas mai nauyin kilogiram 12.5 wasu kuma na karbar N13,500.
Wasu daga cikin kwastomomin da suka zanta da Aminiya sun koka da cewa karin farashin gas din na kawo cikas ga kasafin kudinsu da kuma haifar da barazana ga kasuwancinsu.
Karancin gas din ba zai jima ba —NALGAM
Shugaban kungiyar masu sayar da gas ta Najeriya (NALGAM), Oladapo Olatunbosun, a tattaunawarsa da Aminiya, ya ce karancin gas din na wucin gadi ne.
Ya alakanta lamarin da lalacewar wani jirgin ruwa dauke da tan 14,000 na gas din akan hanyarsa ta zuwa Legas a gabar teku.
Ya kuma bayyana faruwar lamarin a matsayin abin takaici, yayin da ’yan kasuwa ke kukan tashin farashin kayayyaki.