✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisbah ta kori jami’inta kan hada kai da masu badala a Kano

Daurawa na neman korarren hafsan Hisbah ruwa a jallo kan hada kai da bata-gari da taimaka wa masu badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kori daya daga cikin hafsoshintta da ta samu da laifin yi mata zagon kasa a aikin da take yi na kawar da badala a jihar.

Babban Kwamandan Hukumar Hisbah Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa hukumar na neman korarren hafsan Hisbar ruwa a jallo, kan laifin hada kai da bata-gari wajen taimaka wa masu ayyukan barna a jihar.

Sheikh Aminu Daurawa ya kara da cewa Hukumar na binciken wasu ma’aikatan nata su biyar da ake zargi da sa hannunsu a cikin wannan badakala.

Daurawa ya bayyana cewa “mun kori Mataimakin Sufurtanda na Hisbah (DSH) inda kuma muke neman sa ruwa a jallo. A duk lokacin da muka same shi, to za mu kama shi tare da gurfanar da shi gaban kuliya.

“Abin da yake yi shi ne yana hada baki da masu otel-otel don kada a kai wa otel dinsu sumame.

“To lokacin da muka kai suname irin wadannan otel sai suka ji haushi cewa bayan sun biya shi kudi, ga kuma abin da ya faru.

“Akwai wani ma a cikinsu da ya ce mana mu gaya masa duk abin da muke so zai taimaka mana; Mun gaya masa cewa gwamnati ce ta dora mana nauyin gudanar da wannan aiki da muke yi.”

Shaikh Daurawa ya kara da cewa “ba mu zuwa kowane sumame sai mun bi wasu matakai, bayan mutanen unguwa sun aiko mana da takardar sanarwa game da abin da ke faruwa a kusa da su tare da sa hannun akalla mutane biyar daga unguwar.

“Sai mun tura masu yi mana binciken sirri don mu gano gaskiyar abin da aka sanar da mu. Sannan sai mu sanar da DPO na yankin sannan sai mu sami takarar iznin shiga wurin.