Ana zargin wani matashi mai suna Abdulazeez Idris da kashe ’yar uwarsa mai shekara 6, Aisha Saidu a Unguwar Juma da ke garin Zariya a Jihar Kaduna.
Aminiya ta ruwaito cewa, mahaifin yarinyar, Saidu Dahiru ya yi wa ’yan sanda korafin cewa ’yarsa da ake nema aka rasa ba ta dawo gida ba bayan tafiyarta makarantar Islamiyyar.
- ’Yan Nijeriya za su ci moriyar sauye-sauyen haraji da muka kawo — Shettima
- Mai ’ya’ya 12 ya mutu a ɗakin karuwarsa
Malam Saidu ya yi zargi cewa, Abdulazeez wanda da ne a wurinsa shi ne ya yi garkuwa da ’yarsa.
Ya bayyana cewa, da farko wani da bai san kowane ne ba ya kira shi a waya yana neman kudin fansar ’yarsa har naira miliyan takwas muddin yana son a dawo masa da ita cikin aminci.
Kazalika, cikin wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan ya fitar, ya ce tuni jami’ansu sun cika hannu da matashin da ake zargi.
ASP Mansir ya ce sun kama matashin Abdulazeez Idris a Karamar Hukumar Makarfi ta jihar yayin da a halin yanzu sashen kula da laifukan garkuwa da mutane ke bincike a kan lamarin.
Sanarwar ta ce matashin ya bayyana wa ’yan sandan yadda ya yi wa yarinyar yankan rago bayan ta gane shi.
Kakakin ’yan sandan ya ce matashin ya ce ya yi wa yarinyar yankar rago da reza ne sannan ya jefar da gawarta a cikin wata rijiya.
Ya kara da cewa, Kwamishinan ’yan sandan Kaduna,CP Audu Ali Dabigi, ya bai wa al’umma tabbacin bin diddigin lamarin cikin tsanaki domin tabbatar da an bi wa yarinyar da iyayenta hakkinsu.
Nan gaba kadan za a miƙa matashin kotu da zarar ’yan sanda sun kammala bincike.