kungiyar direbobi ta kasa (NURTW) ta bukaci gwamnatin tarayya ta kawo karshen gudanar da garejin kan titi, sannan ta taimaka wajen kafa ginannu a yardaddun wurare.
Shugaban kungiyar, Alhaji Najeem Usman Yasin ne ya yi kiran a lokacin da yake tsokaci kan tashin bam din Nyanya da ke yankin Abuja, inda mutane da dama su ka rasa ransu, wasu suka ji rauni.
Shugaban ya ce baya ga matsaloli da ake samu daga masu lodi a gefin titi, wuraren na kawo cunkoso ababen hawa da na jama’a, al’amarin da yakr babban hadari ne.
Ya ce kungiyarsa a shirye take ta hada kai da kananan hukumomi da ke da hurumin gudanar da tashoshin mota, wajen zaben wuri da raya shi don inganta samun kudin shiga zaman lumana ga kasa.
Alhaji Najeem ya ce kungiyar ta rasa mambobi a yayin tashin bam, baya ga wadanda suka tsira da raunuka, sai kuma motoci da suka kone. Ya bukaci jama’a da su fifita shiga mota a gareji don karfafa musu gwiwa, sannan ya bukaci shugabannin tashoshi mota a duk fadin kasar nan su kara azama wajen tabbatar da tsaro ta hanyar kawar da motocin da ba sa aiki, sannan kuma da sa ido a kan mutane da ke hulda da wajen don tabbatar da tsaro.
Ta bangaren tsare-tsaren kungiyar don kyautata wa direbobi da fasinja, shugaban ya ce akwai tsarin RAIS da suke gudanarwa, inda ake bukatar kowane fasinja ya rubuta sunansa da na makusantansa a gareji, don sada shi ga dangin, idan wani abu ya bijiro, baya ga Naira 40,000 da ake bayarwa don jinya idan fasinja ya yi rauni, ko Naira dubu 150 da za a ba iyalansa, idan ya rasu.
Garejin kan titi na tattare da fitinu -Najeem Yasin
kungiyar direbobi ta kasa (NURTW) ta bukaci gwamnatin tarayya ta kawo karshen gudanar da garejin kan titi, sannan ta taimaka wajen kafa ginannu a yardaddun…