✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Garba Shehu na wuce gona da iri – Aisha Buhari

Mai dakin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta bayyana wasu kalamai masu zafi da ake ta tafka muhawara a shafukan sada zumunta game da…

Mai dakin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta bayyana wasu kalamai masu zafi da ake ta tafka muhawara a shafukan sada zumunta game da mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu.

An dai wallafa rubutun ne mai taken “Garba Shehu na wuce gona da iri”, wanda mai dakin shugaba Buharin ta nuna yadda mai magana da yawun mijin nata ke ‘yi wa iyalan shugaban zagon kasa’.

Aisha ta laburta cewa lokacin da aka shirya kaidin bidiyon da diyar Mamman Daura ta yada a yanar gizo inda ake kokarin fahimtar da ‘yan Najeriya cewa an hanata shiga fadar shugaban kasa lokacin da ta dawo Najeriya bayan dogon hutun da ta dauka, Garba Shehu ya yi shiru duk da cewa ya san gaskiyar lamarin maimakon karyata labarin.