An shafe shekaru aru-aru ana takaddama kan ganin watan azumi da na Sallah, kuma duk da cigaban zamani tsugune ba ta kare ba.
Wasu ba sa yarda idan ganin watan ya zo daidai da hasashen masana kimiyya, wasu kuma na ganin dole ganin ya zo daidai da hasashen masanan.
A bangare guda kuma, akwai wadanda ke cewa sai sun ga watan da kansu, akwai kuma masu ra’ayin cewa ganin watan Saudiyya ya kamata kowa ya bi.
Domin warware zare da abawa kan yadda abin yake, ga bayanin matakan duban wata da yadda ake tantancewa har zuwa yadda Sarkin Musulumi ke sanarwa.
Aminiya ta tattauna ne da Malam Yahaya Muhammad Boyi, Sarkin Malaman Sakkwato, Mamba a Kwamitin Ganin Wata na Kasa, Mashawarcin Sarkin Musulmi Kan Harkokin Addini.