✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganin bayan matsalar tsaro Tinubu ya sa a gaba — Shettima

A shekaru 20 da suka gabata, Arewacin Najeriya na fama da kalubale iri-iri na tsaro.

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya ce kawo karshen tashe-tashen hankula a kasar nan da matsalar tsaro ke haddasawa, ita ce babbar ajandar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Shettima ya bayyana hakan ne a jawabinsa yayin bude taron kwanaki biyu kan matsalar tsaro a Arewacin Najeriya, mai taken: “Hanyar magance matsalar tsaro a Arewacin Najeriya” wanda gamayyar kungiyoyin Arewa (CNG) ta shirya a Abuja ranar Laraba.

Shettima, wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban ma’aikatan ofishinsa, Sanata Ibrahim Hassan, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin tarayya ba ta ja da baya wajen magance matsalar tsaro a cikin al’umma, ya kuma yi kira da a hada kai wajen dakile wannan matsala.

“Na yi imanin taro irin wannan da jama’a suka hallara a nan guda ne cikin ire-iren alkawuran da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa al’ummar kasar a jawabinsa na farko bayan kama mulki, inda ya bayyana cewa kawo karshen matsalar tsaro shi ne babbar ajandar gwamnatinsa.

“Don haka ba mu wasa da rawar da tsaro ke takawa a harkokin mulki ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa aka ware kaso mafi girman kasafin kudi ga bangaren tsaro. Ina so in yi kira ga dukkanin wadanda lamarin shafa da masu ruwa da tsaki da su taka rawar da ta kamace su a wannan aiki,” in ji shi.

A nasa jawabin, Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya bukaci ‘yan Najeriya a kan kada su karaya dangane da halin da aka tsinci a kai a yanzu.

A cewarsa, za a iya samun nasara a yaki da rashin tsaro amma dole ne al’umma ta rungumi aiwatar da tsare-tsare da manufofinta.

“An sha yin maganganu da yawa game da rashin tsaro a Arewa da Najeriya baki ɗaya amma kada mu yanke kauna.

“Wannan ba bigiren da za a yi magana kan batun hanyoyin ba ne, domin kamar yadda muke magana su ma ‘yan fashin dajin sun kasa kunne suna jinmu, amma su sani mun fi su damuwa da talakawan da muke mulkinsu.

“Dole ne mu samar da zaman lafiya a Arewa. Mun yi ta fafutukar ganin an samu zaman lafiya, amma yanzu dole ne mu nemo hanyar da za mu bi, kuma mu mayar da hankali kan hanyoyin da za mu iya shawo kan wadannan matsalolin.

“Abin da ya rage mana a yanzu shi ne aiwatarwa, kuma kamar yadda na shaida wa kwamitin CNG da suka ziyarce ni a Sakkwato cewa dole ne mu nemo tsarin aiwatar da aiki kuma wannan bai kamata ya zama wani taron tattaunawa ba,” in ji shi.

Ko’odinetan CNG na kasa, Kwamared Jamilu Aliyu Charanchi, ya ce rashin sanya al’umma da hadin kai tsakanin hukumomin tsaro su ne ababen da ke kara rura wutar rashin tsaro a Najeriya.

Ya ce: “A shekaru 20 da suka gabata, Arewacin Najeriya na fama da kalubale iri-iri na tsaro.

“Barazanar da ke kara ta’azzara daga kungiyoyin ‘yan tada kayar baya da ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane da sauran ayyukan miyagun laifuka, sun yi mummunan tasiri a rayuwar al’ummarmu.”