✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ni da niyyar mayar da Legas babban birnin Najeriya — Tinubu

Bai kamata ɗauke Hukumar FAAN daga Abuja zuwa Legas ta ɗauki hankalin jama’a ba.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce ba shi da niyyar ɗauke babban birnin tarayyar ƙasar daga Abuja zuwa Legas.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, ya ce masu jita-jita ne ke yaɗa maganar domin jan hankalin al’umma gare su.

“An soma watsa wannan jita-jitar a lokacin yaƙin neman zabe a bara inda ƴan adawa ke neman duk wasu hanyoyi na daƙile shi.”

Wannan na zuwa ne bayan matakin da Gwamnatin Tarayyar ta ɗauka na mayar da wasu ɓangarori na Babban Bankin Najeriya CBN da kuma Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama FAAN daga Abuja zuwa Legas.

Lamarin da ya janyo ƙorafi da kiraye-kiraye daga wasu ƙungiyoyi na wasu ɓangarorin ƙasar, inda suka yi zargin cewa tamkar wani mataki ne aiwatar da wata manufa ta daban.

Onanuga ya ce matakin mayar da wani sashi na FAAN bai kamata ya ja hankalin mutane da yawa ba saboda Jihar Legas ita ce cibiyar kasuwanci kuma cibiyar sufurin jiragen sama a Najeriya, saboda haka ya ce har yanzu FAAN za ta ci gaba da kasancewa a Abuja.

Ya kuma bayar da misali kan cewa akwai ma’aikatun Gwamnatin Tarayya da hedikwatarsu ba a Abuja take ba, wadanda suka hada da NIMASA da NPA ke Legas haka kuma akwai NIWA da ke Lokoja.

“Akwai ma’aikatu da yawa da ba a Abuja suke ba dangane da aikinsu kamar NIMASA da take Legas. Haka kuma NPA da kuma Hukumar Kula da Sufurin Ruwa (NIWA) da ke Lokoja.”

Sanarwar dai ta ƙara da cewa bai kamata a siyasantar da lamurran gwamnati ba.