✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gani Ya Kori Ji: Hotunan muhimman abubuwan da suka faru a wannan makon

Gani Ya Kori Ji: Hotunan muhimman abubuwan da suka faru a wannan makon

Gani Ya Kori Ji na Aminiya ya tattaro muku hotunan wasu muhimman abubuwan da suka faru a wannan mako da muke bankwana da shi domin kayatar da ku.

A sha kallo lafiya:

Yadda aka gudanar da taron tattaunawa na rukunin kamfanin Media Trust karo na 20 inda aka bi diddigin manufofin manyan ’yan takarar Shugaban Kasa a zaben 2023.

Yadda Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi A. Sule ya halarci jana’izar babban dansa da ya rasu ranar Juma’a da dare a garinsu na Gudi da ke Karamar Hukumar Akwanga.

Yadda Shugaban Kasa Buhari ya sauka a Katsina bayan ya dawo daga taron kasa da kasa akan sha’anin noma da aka yi a kasar Senegal a ranar Alhamis.

Fusatattun matasa sun lalata allon da Buharin ya kaddamar da aiki a Katsina, kuma sun jefi ayarinsa, wasu kuma suka yi masa ihun ‘ba ma so’.

 

Matasan da suka fasa allon a Katsina
Matasan da suka fasa allon a Katsina
Buhari a Katsina
Buhari a Katsina

Yadda jirgin kasan Abuja Kaduna ya yi hatsari a hanyar zuwa Abuja bayan ya taso daga Kaduna.