Daga cikin abubuwan da suka faru a wannan makon mai karewa akwai shagulgulan da aka gudanar na Babbar Sallah – da ma wadanda suka gabace ta ko suka biyo baya.
Ga kuma tsallake rijiya da baya da wani matukin jirgin saman yaki na Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ya yi a lokacin da ‘yan bindiga suka kakkabo jirgin da yake ja.
Ga kadan daga cikin abubuwan da suka faru a cikin hotuna.
![Flight Lieutenant Abayomi Dairo and the Chief of Air Staff pic Idowu Isamotu Filait Laftanar Abayomi Dairo, matukin jirgin saman yakin da 'yan bindiga suka kakkabo, tare da Babban Hafsan Sojin Sama na Najeriya Isiaka Oladayo Amao. Ranar Lahadi 18 ga watan Yuli Dairo ya tsallake rijiya da baya lokacin da aka harbo jirgin saman yakin da yake ciki a Jihar Zamfara (Hoto: Idowu Isamotu)](https://i0.wp.com/aminiya.ng/wp-content/uploads/2021/07/Flight-Lieutenant-Abayomi-Dairo-and-the-Chief-of-Air-Staff-pic-Idowu-Isamotu.jpeg?w=350&h=233&ssl=1)
Filait Laftanar Abayomi Dairo, matukin jirgin saman yakin da ‘yan bindiga suka kakkabo, tare da Babban Hafsan Sojin Sama na Najeriya Isiaka Oladayo Amao. Ranar Lahadi 18 ga watan Yuli Dairo ya tsallake rijiya da baya lokacin da aka harbo jirgin saman yakin da yake ciki a Jihar Zamfara (Hoto: Idowu Isamotu)