✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje zai ba Kwankwaso sarautar mahaifinsa

Gidan nan ya cancanci dukkan alheri da girmamawarmu, inji Ganduje

Gwamnan Kano, Abudullahi Ganduje ya bayyana aniyarsa ta ba da sarautar Makaman Karaye ga gidan su tsohon maigidansa kuma tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin ta’aziyyar da ya je mahaifar Kwankwaso bayan rasuwar mahaifin tsohon gwamnan, wanda shi ne Makaman Karaye kafin rasuwarsa a gidansa da ke garin.

“Ba sai an nemi hakan ba, saboda wannan gida ya cancanci komai a daga wurinmu kuma a koyaushe muna daraja shi,” inji gwamnan wanda yanzu yake zaman doya da manja da Sanata Kwankwaso.

Ya bayyana hakan ne bayan kanen Sanata Kwankwaso, Alhaji Baba Musa Kwankwaso, wanda shi ne Dagacin garin, ya bukaci a bar sarautar Madakin ta ci gaba da kasancewa a gidan.

Ganduje ya ce, “Dole ne mu ba da muhimmanci da cikakkiyar kulawa ga duk abin da ya shafi wannan babban gida, saboda matsayin baba da kuma Dagaci.”

Ya yi bayanin ne bayan Alhaji Baba ya yaba da karamcinsa ga iyalan mamacin, wanda ya ce ya dauki gwamnan tamkar dan cikinsa da ya haifa.

“Mai girma Gwamna muna rokon ka taimaka kar sarautar mahaifinmu ta Makaman Karaye ta bar gidan. Muna neman goyon bayanka yadda aka saba.

“Na wakilci mahaifinmu a lokacin da yake Dagaci sannan kuma na wakilce shi a lokacin da yake hakimi na tsawon shekara 20,” a cewarsa.

Tabbacin barin sarautar a gidan da Ganduje ya bayar ya sa ake ganin zai ba da ita ce ga Alhaji Baba, duk da cewa Sanata Kwankwaso ne wa.

Kwamishinan Raya Karkara kuma dan uwan Sanata Kwankwaso, Musa Iliyasu Kwankwaso, ne ya fara tarbar gwamnan sannan suka karasa zuwa ga Dagacin a gidan mamacin.

Alhaji Baba ya bayyana jin dadin iyalan da ziyarar ta’aziyyar, yana mai cewa, “Muna fatar kaunar da ke tsakaninmu da ku da kuma mahaifinmu za ta dore bayan rasuwarsa.

“Mun san baba ya dauke ka tamkar dan cikinsa, muna fata kai ma za ka rike mu kamar ’ya’yanka,” inji kanen Kwankwaso.

Da yake ta’aziyya, gwamnan ya ce, “Babanmu dattijo ne, mutum mai hakuri da adalci kuma ya jajirce wurin yi wa al’umma hidima shi ya sa jama’arsa da ma a wasu wuraren ake ambaton sa da alheri.

“Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya kuma sanya shi a Jannatul Fiddaus.”