✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ganduje ya yi wa fursunoni 12 afuwa kwanaki uku kafin zabe

NNPP na zargin Ganduje zai yi amfani da ’yantattun fursunoni wajen hargitsa zaben gwamna a Kano.

Kwanaki uku kafin zaben gwamnoni da ’yan majalisar dokoki, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya yi afuwa wa wasu fursunoni 12 da aka tabbatar wa hukuncin kisa kuma tuni shida daga cikinsu an zartar musu da hukuncin daurin rai da rai.

Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Yari (NCS) reshen Jihar Kano, SC Musbahu Lawan Nassarawa ya fitar a wannan Talatar.

Kungiyoyin kwadago sun shiga yajin aiki a Faransa

INEC ta dakatar da Kwamishinan Zaben Sakkwato

A cewar SC Lawan, Ganduje ya kuma yi afuwa ga wasu fursunoni mata guda hudu da ke cin sarka ta tsawon lokaci bayan samunsu da kyawawan dabi’u kamar yadda Hukumar NCS din ta bayar da dama.

Kazalika, Ganduje ya bai wa fursunonin da ya ’yantar kyautar naira dubu biyar-biyar domin su yi guzurin komawa gida wajen ’yan uwansu.

Jami’in ya ce Shugaban Kwamitin Yi wa Masu Laifi Afuwa, Abdullahi Garba Rano da kuma Kwanturolan Gidajen Yarin Kano, Sulaiman Muhammad Inuwa, sun yaba wa Ganduje dangane da yadda ya ribaci ikon da Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya ba shi na ’yantar da fursunonin da aka samu da halayya ta gari yayin zamansu a gidan kaso.

“Inuwa ya bayyana ’yantattun fursunonin a matsayin jakadu nagari na Gidajen Yarin Najeriya. Yana kuma gargadinsu da su kauracewa fadawa cikin duk wani laifi da ka iya mayar da su inda suka fito. ”

Bayanai sun ce wadansu daga cikin ’yantattun fursunonin sun shafe fiye da shekaru 25 suna jiran a zartar musu da hukunci.

A wata tattanawa da nadar murya da aka yi da wasu daga cikinsu, wani mai shekara 69, ya ce ya shafe fiye da shekaru 23, amma a yanzu babu abin da zai yi face godiya ga gwamna da kuma mahukuntan gidan gyaran halin da suka yi ruwa da tsaki wajen ’yantar da shi.

NNPP na zargin Ganduje da shirya wa zabe makarkashiya

Ita kuwa jam’iyyar NNPP ta bakin wani jigonta, Baffa Bichi ta ce suna sane da shirin da gwamnatin Ganduje ta yi na kawo bakin ’yan daba daga kasashen Nijar da Chadi cikin jihar don ganin sun tayar da tarzoma tare da kawo cikas a zaben gwamna da ke tafe.

Dokta Bichi ya kara da cewa, Gwamna Ganduje bai tsaya a nan ba, sai da ya yi kokarin ganin ya yi afuwa ga wasu kasurguman ’yan daba a jihar wadanda aka yanke musu hukuncin kisa don su yi masa aiki a ranar zaben.

“Gwamnatin Kano ta yi afuwa ga tantiran ’yan daba wadanda ke zaman jiran sakamakon yanke musu hukuncin kisa.

“Haka kuma tana kokarin fito da wasu ’yan dabar da ke wasu gidajen yarin a fadin kasar nan.

“Babban misalin shi ne yadda ta fito da wani mai suna Muhammad Abbas mai lambar kurkuku K/35c/2008 daga gidan kurkuku na Jihar Neja.

Sai dai Kwamishinan Labarai na Kano, Muhammad Garba, ya musanta zargin yana mai cewa Ganduje ya yi fursunonin afuwa ne ba da wata manufa ba face ribatar ikon da Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya ba shi na idan bukatar hakan ta taso.

Kwamishinan ya kara da cewa, jam’iyyar NNPP na wannan zargin ne kawai saboda fargabar ba za ta yi nasara ba a zaben gwamna da na ’yan majalisar dokoki da za a gudanar a karshen wannan mako.

Ana iya tuna cewa, a wata hira da Ganduje ya yi da Gidan Talabijin na Trust a shekarar 2021, ya bayyana cewa gwamnoni na tsoron sanya hannu kan hukuncin kisa ga wadanda aka yankewa hukuncin “saboda ba sa son a aiwatar da hukuncin kisa daga baya kuma suka gano wanda aka zartarwa hukuncin bai cancanci hakan ba.”