Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya taya tsohon mai gidansa kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso murnar cika shekaru 64 da haihuwa.
Ganduje ya aike da Kwankwaso sakon da sa hannunsa a jaridun kasar nan na ranar Laraba 21 ga Oktoba, wanda ya zo daidai da ranar da kwankwason ke cika shekara 64 a duniya.
Alakar siyasa tsakanin Kwankwaso da Ganduje mai tsawon tarihi ce kafin su raba gari a watan Maris na shekarar 2016.
Kafin zaman Ganduje gwamna a 2015, shi ne mataimakin gwamnan Kwankwaso a kakar zabe 1999 da kuma 2011.
A lokacin mulkin Kwankwaso karo na farko, ya Samar da Jami’ar kimiyya da fasaha ta dake garin Wudil, Inda a zangonsa na biyu a 2011 ya kafa Jami’ar Arewa maso Yamma, wadda yanzu aka sauya sunanta zuwa Jami’ar Yusuf Maitama Sule.