✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya shirya wa zaben Kano makarkashiya —NNPP

Gwamnatin Kano da jam’iyyar APC sun ce ba za su kyale NNPP ta musu magudi ba.

Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ta zargi Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da shirya mata makarkashiya don ganin ba ta kai ga samun nasarar zaben gwamna a jihar ba.

Jigo a jam’iyyar kuma wanda ya yi takarar Sanatan Kano ta Arewa a zaben da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu, Dokta Baffa Bichi ne ya bayyana haka a yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Baffa Bichi ya ce suna sane da shirin da gwamnatin Ganduje ta yi na kawo bakin ’yan daba daga kasashen Nijar da Chadi cikin jihar don ganin sun tayar da tarzoma tare da kawo cikas a zaben gwamna da ke tafe.

Dokta Bichi ya kara da cewa, Gwamna Ganduje bai tsaya a nan ba, sai da ya yi kokarin ganin ya yi afuwa ga wasu kasurguman ’yan daba a jihar wadanda aka yanke musu hukuncin kisa don su yi masa aiki a ranar zaben.

“Gwamnatin Kano ta yi afuwa ga tantiran ’yan daba wadanda ke zaman jiran sakamakon yanke musu hukuncin kisa.

“Haka kuma tana kokarin fito da wasu ’yan dabar da ke wasu gidajen yarin a fadin kasar nan.

“Babban misalin shi ne yadda ta fito da wani mai suna Muhammad Abbas mai lambar kurkuku K/35c/2008 daga gidan kurkuku na Jihar Neja.

A cewarsa, suna sane da yadda Gwamna Ganduje yake shige da fice wajen kawo cikas a zaben gwamna inda yake so Hukumar INEC ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.

“Gwamnatin Ganduje ta hada kai da baragurbin jami’an tsaro da ma’aikata INEC na wucin-gadi wajen jinkirta yin zabe akan lokaci da rikirkita kayayyakin zabe da lalata sakamakon zaben.

“Irin wannan abin ne suka yi amfani da shi a lokacin Zaben 2019, inda wasu jiga-jigan jam’iyyar APC suka shiga wurin da ake tattara sakamakon zabe a Karamar Hukumar Nassarawa suka yayyaga sakamakon zabe har aka ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba wanda a karshe suka shiga suka fita suka kwace mana kujera.

“Muna kira ga Hukumar INEC da masu sa ido a zabe da su san abin da ake ciki don daukar matakin da ya dace.

“Muna so jama’a su sani cewa ba za mu sake yarda wani ya zo ya sake kwace musu kujera kamar yadda aka yi a 2019 ba.

“Muna sane cewa duk kokarin da Ganduje ya yi na samun hadin kan Sufeton Yan sanda ya ci tura.

A cewar Dokta Baffa, “muna sane da yadda Ganduje yake amfani da sunan Shugaban Buhari yana bin ofisoshin jami’an tsaro don neman hadin kansu.

Dokta Baffa Bichi ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ba za ta lamunci duk wani lamari da ka iya janyo wa zaben gwamna cikas daga jam’iyya mai mulki.

“Duk da cewa mu mutane ne masu son zaman lafiya a wancan lokaci mun hana magoya bayanmu fitowa don yin zanga-zanga amma a wannan karon hakurinmu ya kare ba za mu hana su yin duk abin da suka ga dama ba matukar aka maimaita abin da ya faru a 2019.

Jam’iyyar NNPP ta yi kira ga Shugaba Muhammad Buhari da ya san halin da Gwamna Ganduje ke kokarin jefa Jihar Kano a ciki.

Ba za mu kyale NNPP ta yi mana magudi ba — Gwamnatin Kano

Sai dai a martaninta, Gwamnatin Jihar Kano ta bakin Kwamishinan Watsa Labarai, Kwamared Muhammad Garba ta bayyana cewa duk zarge-zargen da jam’iyyar NNPP ke yi ba su da tushe ballantana makama.

“Abin da suke fadi abubuwa ne da suke da niyyar aikatawa don sanin cewa muna bibiyarsu ya sanya suke wannan babatu.

“To mu a shirye muke duk abin da suke shiryawa a tafin hannunmu yake.

A cewar Muhammad Garba, “mu dai matakin da muka dauka shi be ba za mu taba barinsu su yi mana magudi ba kamar yadda suka yi a shekarar 2019 ba inda suka sa matasa suka rika yin zabe ba tare da katin zabe ba, lamarin da ya janyo har sai da aka gudanar da wani dan kwarya-kwaryar zaben.

Kwamishinan ya yi kira ga hukumomin tsaro da su sa ido wajen ganin sun bankado ire-iren mutanen da jam’iyyar NNPP ta kawo don tayar da zaune tsaye a lokacin zaben gwamna da ke tafe.

A ranar 11 ga watan Maris ne dai za a gudanar da zaben gwamnoni da ’yan majalisar dokoki na jihohi.