✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ganduje ya nada Ishaq Sidi Ishaq a matsayin mai ba shi shawara

Gwamnan dai ya nada Ishaq ne a matsayin Babban Hadiminsa kan  harkokin kirkira.

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya nada darakta a masana’antar Kannywood, Ishaq Sidi Ishaq mukamin babban mai ba shi shawara.

Gwamnan ya nada Ishaq ne a matsayin Babban Hadiminsa kan  harkokin kirkira wato Creative Industry a turance.

Fitaccen Darakta a masana’antar ta Kannywood, Falalu Dorayi ne ya bayyana hakan, inda ya ce, “Muna taya darakta Ishaq Sidi Ishaq murnar samun matsayin Senior Special Assistant (babban Mai Ba Da Shawara) ga Gwamnan Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje a bangaren kirkira; Akwai kalubale, sai ka yi da gaske. Domin tukunyar sama ce ragamarta ta dawo hannunka. Allah Ya ba ka ikon aiki da adalci.”

Ishaq Sidi Ishaq dai jarumi ne kuma Darakta da aka dade ana damawa da shi a masana’antar Kannywood, duk da cewa yanzu ba a cika jin duriyarsa ba, amma har yanzu yakan fito a fim jefi-jefi.

%d bloggers like this: